Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Neh 11:23-36 Littafi Mai Tsarki (HAU)

23. Sarki ya yi wa shugabannin mawaƙa umarni da ƙarfi a kan abin da za su yi kowace rana.

24. Fetahiya ɗan Meshezabel, daga zuriyar Zera na kabilar Yahuza, shi ne wakilin sarki a kan dukan abin da ya shafi jama'a.

25. Game da ƙauyuka da gonakinsu kuma, waɗansu mutanen Yahuza suka zauna a Kiriyat-arba, da Dibon da ƙauyukanta, da Yekabzeyel da ƙauyukanta,

26. da a biranen Yeshuwa, da Molada, da Bet-felet,

27. da Hazar-shuwal, da Biyer-sheba da ƙauyukanta,

28. da Ziklag, da Mekona da ƙauyukanta,

29. da En-rimmon, da Zora, da Yarmut,

30. da Zanowa, da Adullam da ƙauyukansu, da Lakish da gonakinta, da Azeka da ƙauyukanta. Haka suka yi zango daga Biyer-sheba zuwa kwarin Hinnom.

31. Mutanen kabilar Biliyaminu suka zauna a Geba, da Mikmash, da Ayya, da Betel da sauran ƙauyuka na kewaye,

32. da Anatot, da Nob, da Ananiya,

33. da Hazor, da Rama, da Gittayim,

34. da Hadid, da Zeboyim, da Neballat,

35. da Lod, da Ono, wato kwarin masu sana'a.

36. Waɗansu kashi na Lawiyawan da suke a Yahuza, aka sa su zauna a yankin ƙasar Biliyaminu.

Karanta cikakken babi Neh 11