Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Neh 11:20-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Sauran jama'ar Isra'ila kuwa, da firistoci, da Lawiyawa suka zauna a dukan garuruwan Yahuza, kowa ya zauna a gādonsa.

21. Amma ma'aikatan Haikali suka zauna a Ofel. Ziha da Gishfa, su ne shugabannin ma'aikatan Haikali.

22. Shugaban Lawiyawan da yake a Urushalima, shi ne Uzzi ɗan Bani, jīkan Hashabiya. Sauran kakanninsa su ne Mattaniya, ɗan Mika daga zuriyar Asaf. Su ne mawaƙa a Haikalin Allah.

23. Sarki ya yi wa shugabannin mawaƙa umarni da ƙarfi a kan abin da za su yi kowace rana.

24. Fetahiya ɗan Meshezabel, daga zuriyar Zera na kabilar Yahuza, shi ne wakilin sarki a kan dukan abin da ya shafi jama'a.

25. Game da ƙauyuka da gonakinsu kuma, waɗansu mutanen Yahuza suka zauna a Kiriyat-arba, da Dibon da ƙauyukanta, da Yekabzeyel da ƙauyukanta,

26. da a biranen Yeshuwa, da Molada, da Bet-felet,

27. da Hazar-shuwal, da Biyer-sheba da ƙauyukanta,

28. da Ziklag, da Mekona da ƙauyukanta,

29. da En-rimmon, da Zora, da Yarmut,

30. da Zanowa, da Adullam da ƙauyukansu, da Lakish da gonakinta, da Azeka da ƙauyukanta. Haka suka yi zango daga Biyer-sheba zuwa kwarin Hinnom.

Karanta cikakken babi Neh 11