Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Neh 10:28-34 Littafi Mai Tsarki (HAU)

28. Jama'ar Isra'ila, da firistoci, da Lawiyawa, da masu tsaron ƙofofi, da mawaƙa, da ma'aikatan Haikali, da dukan waɗanda suka ware kansu daga sauran al'umman waɗansu ƙasashe, domin su bi dokokin Allah, su da matansu, da 'ya'yansu mata da maza, da dai duk waɗanda suke da sani da fahimta,

29. suka haɗa kai da 'yan'uwansu, da shugabanninsu, suka rantse, cewa la'ana ta same su idan ba su kiyaye dokokin Allah waɗanda ya ba bawansa Musa ba. Suka rantse za su kiyaye, su aikata umarnai, da ka'idodi, da dokokin Ubangijinmu.

30. Suka ce, “Ba za mu aurar wa mutanen ƙasar da 'ya'yanmu mata ba. Ba kuma za mu auro wa 'ya'yanmu maza 'ya'yansu mata ba.

31. “Idan kuma mutanen ƙasar sun kawo kayayyaki da hatsi don sayarwa a ranar Asabar, ba za mu saya ba, ko kuma a wata tsattsarkar rana.“A kowace shekara ta bakwai ba za mu girbe amfanin gonakinmu ba, za mu kuma yafe kowane irin bashi.

32. “Muka kuma anita kowannenmu zai riƙa ba da sulusin shekel a shekara domin aikin Haikalin Allahnmu.

33. “Za mu tanadi gurasar ajiyewa, da hadayar gāri ta kullum, da ta ranakun Asabar, da ta amaryar wata, da ta ƙayyadaddun idodi, da abubuwa masu tsarki, da hadaya don zunubi saboda yi wa jama'ar Isra'ila kafara, da dukan aiki na Haikalin Allahnmu.

34. “Muka kuma jefa kuri'a wato firistoci, da Lawiyawa, da jama'a a kan kawo itacen hadaya a Haikalin Allahnmu, bisa ga gidajen kakanninmu, a kan ƙayyadaddun lokatai a shekara, don a ƙona hadayu a bisa bagaden Ubangiji Allahnmu, kamar yadda aka rubuta a dokoki.

Karanta cikakken babi Neh 10