Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Nah 3:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Kaiton birnin jini,Wanda yake cike da ƙarairayi daganima,Da waso kuma ba iyaka!

2. Ku ji amon bulala da kwaramniyarƙafafu,Da sukuwar doki da girgizar karusai!

3. Sojojin dawakai suna kai sura,Takuba suna walƙiya, māsu sunaƙyalƙyali.Ga ɗumbun kisassu, da tsibingawawwaki,Matattu ba su ƙidayuwa,Suna tuntuɓe a kan gawawwaki!

4. Ya faru saboda yawan karuwancinNineba kyakkyawa mai daɗinbaki,Wadda ta ɓad da al'umman duniyada karuwancinta,Ta kuma ɓad da mutane da daɗinbakinta.

5. Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Inagāba da ke,Zan kware fatarinki a idonki,Zan sa al'ummai da mulkoki su dubitsiraicinki.

6. Zan watsa miki ƙazanta,In yi miki wulakanci,In maishe ki abin raini.

Karanta cikakken babi Nah 3