Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Nah 3:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Kaiton birnin jini,Wanda yake cike da ƙarairayi daganima,Da waso kuma ba iyaka!

2. Ku ji amon bulala da kwaramniyarƙafafu,Da sukuwar doki da girgizar karusai!

3. Sojojin dawakai suna kai sura,Takuba suna walƙiya, māsu sunaƙyalƙyali.Ga ɗumbun kisassu, da tsibingawawwaki,Matattu ba su ƙidayuwa,Suna tuntuɓe a kan gawawwaki!

4. Ya faru saboda yawan karuwancinNineba kyakkyawa mai daɗinbaki,Wadda ta ɓad da al'umman duniyada karuwancinta,Ta kuma ɓad da mutane da daɗinbakinta.

5. Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Inagāba da ke,Zan kware fatarinki a idonki,Zan sa al'ummai da mulkoki su dubitsiraicinki.

6. Zan watsa miki ƙazanta,In yi miki wulakanci,In maishe ki abin raini.

7. Dukan waɗanda za su dube kiZa su ja da baya su ce,‘Nineba ta lalace, wa zai yi kukadominta?’A ina zan samo miki waɗanda za suta'azantar da ke?”

8. Kin fi No ne?Wadda take a bakin Nilu,Wadda ruwa ya kewaye ta?Teku ce kagararta.Ruwa ne kuma garunta.

9. Habasha da Masar su ne ƙarfintamarar iyaka,Fut da Libiya su ne kumamataimakanta.

10. Duk da haka an tafi da ita, an kai tacikin bauta.An fyaɗa ƙanananta a ƙasa,An yi kacakaca da su a kowacemararraba.An jefa kuri'a a kan manyanmutanenta,Aka ɗaure dukan manyan mutanentada sarƙoƙi.

11. Ke Nineba kuma za ki bugu,Za a ɓoye ki.Za ki nemi mafaka a wurin maƙiyinki.

Karanta cikakken babi Nah 3