Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Nah 2:3-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Garkuwoyin jarumawansa jajaye ne,Sojojinsa kuma suna saye da mulufi.Da ya shirya tafiya,Karusai suna walƙiya kamarharshen wuta,Ana kaɗa mashi da bantsoro.

4. Karusai sun zabura a tituna ahaukace.Suna kai da kawowa a dandali,Suna walwal kamar jiniya,Suna sheƙawa a guje kamarwalƙiya.

5. Sai aka kira shugabanni,Suka zo a guje suna tuntuɓe,Suka gaggauta zuwa garu,Suka kafa kagara.

6. An buɗe ƙofofin kogi,Fāda ta rikice.

7. An tsiraita sarauniya, an tafi da ita,'Yan matanta suna makoki, sunakuka kamar kurciyoyi,Suna bugun ƙirjinsu.

8. Nineba tana kama da tafki wandaruwansa yake zurarewa,Suna cewa, “Tsaya, tsaya,”Amma ba wanda ya waiga.

9. A washe azurfa!A washe zinariya!Dukiyar ba ta da adadi,Akwai dukiya ta kowane iri.

10. Nineba ta halaka! ta lalace, ta zamakufai!Zukata sun narke, gwiwoyi sunakaɗuwa!Kwankwaso yana ciwo,Fuskoki duka sun kwantsare!

11. Ina kogon nan na zakoki,Inda aka ciyar da 'ya'yan zaki,Inda zaki da zakanya dakwiyakwiyansu sukan tafi,Su tsere daga fitina?

12. Zaki ya kashe abin da ya ishikwiyakwiyansa.Ya kaso wa zakanyarsa abin da yaishe ta.Ya cika kogonsa da ganima.

13. “Ga shi, ina gāba da ke. Ni UbangijiAllah Mai Runduna na faɗa.Zan ƙone karusanki,Takobi kuwa zai karkashe sagarunzakokinki,Zan hana miki ganima a duniya.Ba za a ƙara jin muryoyin jakadunkiba.”

Karanta cikakken babi Nah 2