Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Nah 2:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Wanda yake farfashewa ya aukomaka,Sai ka sa mutane a kagara, a yitsaron hanya,Ka yi ɗamara, ka tattaro ƙarfinkaduka.

2. Gama Ubangiji zai mayar waYakubu da darajarsa kamar taIsra'ila.Ko da masu washewa sun washe su,Sun kuma lalatar da rassan inabinsu.

3. Garkuwoyin jarumawansa jajaye ne,Sojojinsa kuma suna saye da mulufi.Da ya shirya tafiya,Karusai suna walƙiya kamarharshen wuta,Ana kaɗa mashi da bantsoro.

4. Karusai sun zabura a tituna ahaukace.Suna kai da kawowa a dandali,Suna walwal kamar jiniya,Suna sheƙawa a guje kamarwalƙiya.

5. Sai aka kira shugabanni,Suka zo a guje suna tuntuɓe,Suka gaggauta zuwa garu,Suka kafa kagara.

6. An buɗe ƙofofin kogi,Fāda ta rikice.

7. An tsiraita sarauniya, an tafi da ita,'Yan matanta suna makoki, sunakuka kamar kurciyoyi,Suna bugun ƙirjinsu.

Karanta cikakken babi Nah 2