Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Nah 1 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Fushin Ubangiji a kan Nineba

1. Jawabi a kan Nineba ke nan, a littafin wahayin Nahum na Elkosh.

2. Ubangiji Allah mai kishi ne, maisakayya,Ubangiji mai sakayya ne, maihasala.Ubangiji yakan ɗauki fansa a kanmaƙiyansa.Yana tanada wa maƙiyansa fushi.

3. Ubangiji mai jinkirin fushi ne,Mai Iko Dukka.Ubangiji ba zai kuɓutar da mai laifiba.Hanyarsa tana cikin guguwa da cikinhadiri,Gizagizai su ne ƙurar ƙafafunsa.

4. Yakan tsauta wa teku, sai teku taƙafe.Yakan busar da koguna duka.Bashan da Karmel sukan bushe,Tohon Lebanon yakan yanƙwane.

5. Duwatsu sukan girgiza a gabansa,Tuddai kuma su narke.Duniya ta murtsuke a gabansa,Da dukan mazauna a cikinta.

6. Wa zai iya tsaya wa fushinsa?Wa kuma zai iya daurewa dahasalarsa?Yana zuba hasalarsa mai kama dawuta,Duwatsu sukan farfasu a gabansa.

7. Ubangiji mai alheri ne,Shi mafaka ne a ranar wahala.Ya san waɗanda suke fakewa a gareshi.

8. Zai shafe maƙiyansa da ambaliyarruwa,Zai kuma runtumi maƙiyansa zuwacikin duhu.

9. Me kuke ƙullawa game da Ubangiji?Ubangiji zai wofintar da abin nan dakuke ƙullawa,Sau ɗaya kawai zai hallaka ku.

10. Suna maye da abin shansu,Za su ƙone kamar sarƙaƙƙiyar ƙaya,Da busasshiyar ciyawa.

11. Daga cikinki wani ya fito,Wanda ya ƙulla wa Ubangijimakirci,Ya ƙulla shawara marar amfani.

12. Ni Ubangiji na ce,“Ko da yake suna da ƙarfi, sunakuma da yawa,Za a datse su, su ƙare.Ko da yake na wahalar da kai,Ba zan ƙara wahalar da kai ba.

13. Yanzu zan karya karkiyarsa dagawuyanka,Zan kuma tsinke sarƙarta.”

14. Ubangiji ya riga ya yi umarni akanka cewa,“Sunanka ba zai ci gaba ba,Zan farfashe sassaƙaƙƙun siffofiDa siffofi na zubi daga gidangumakanka.Zan shirya maka kabari, gama kairainanne ne.”