Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mika 6:6-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Da me zan zo gaban Ubangiji,In sunkuyar da kaina a gaban Allahna Sama?Ko in zo gabansa da maraƙi banaɗaya domin yin hadaya taƙonawa?

7. Ubangiji zai yi murna da ragunadubbaiKo kuwa da kogunan mai dubbai?Zan ba da ɗan farina ne donlaifina?Ko kuwa zan ba da 'ya'yana sabodazunubina?

8. Ya kai mutum, ya riga ya nunamaka abin da yake mai kyau.Abin da Ubangiji yake so gare ka,shi neKa yi adalci, ka ƙaunaci aikataalheri,Ka bi Allah da tawali'u.

9. Ubangiji yana kira ga birnin.Hikima ce ƙwarai a ji tsoronsunanka.“Ki ji ya kabila, wa ya sa mikilokacinki?

10. Ba zan manta da dukiya ta muguntaa gidan mugu ba,Ba kuwa zan manta da bugaggenmudun awo ba.

Karanta cikakken babi Mika 6