Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mika 2:8-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Ubangiji ya amsa ya ce,“Ba da daɗewa ba mutanena suntashi kamar maƙiyi,Kukan tuɓe rigar masu wucewa dasalama, masu komawa da yaƙi.

9. Kukan kori matan mutanenaDaga gidajensu masu kyau,Kukan kawar da darajata har abadadaga wurin 'ya'yansu.

10. Ku tashi, ku tafi,Gama nan ba wurin hutawa ba ne,Saboda ƙazantarku wadda take kawomuguwar hallaka.

11. “Idan mutum ya tashi yana iskanci,yana faɗar ƙarya, ya ce,‘Zan yi muku wa'azi game da ruwaninabi da abin sa maye,’To, shi ne zai zama mai wa'azinmutanen nan!

12. “Hakika zan tattara ku duka, yaYakubu,Zan tattara ringin Isra'ila.Zan haɗa su tare kamar tumaki agarke,Kamar garken tumaki a makiyayaZa su zama taron jama'a maihayaniya.

13. “Wanda zai huda garu, shi zai yi musujagora,Za su fita ƙofar, su wuce, su fice tacikinta.Sarkinsu zai wuce gabansu,Ubangiji kuma yana kan gaba.”

Karanta cikakken babi Mika 2