Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mal 4:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “Duba rana tana zuwa, sa'ad da dukan masu girmankai, da mugaye za su ƙone kamar tattaka, a ran nan za su ƙone ƙurmus ba abin da zai ragu, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.

2. Amma ku da kuke yi mini biyayya, ikon cetona zai fito muku kamar rana. Zai kawo warkarwa kamar hasken rana. Za ku fita kuna tsalle kamar 'yan maruƙan da aka fisshe su daga garke.

3. Za ku tattake mugaye, gama za su zama kamar ƙura a ƙarƙashin ƙafafunku, a ranan nan da zan aikata, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.

Karanta cikakken babi Mal 4