Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mal 3:12-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Sa'an nan jama'ar dukan al'ummai za su ce ku masu farin ciki ne, gama ƙasarku za ta yi daɗin zama.”

13. “Kun faɗi mugun abu a kaina,” in ji Ubangiji, “Amma kun ce, ‘Me muka ce a kanka?’

14. Kun ce, ‘Ba amfani a bauta wa Ubangiji. Ina amfani a kiyaye abin da ya ce, ko mu yi ƙoƙarin nuna cewa zuciyarmu ta ɓāci saboda ayyukan da muka yi wa Ubangiji Mai Runduna.

15. A ganinmu masu girmankai suna jin daɗi. Masu aikata mugunta kuwa ba arziki kaɗai suke yi ba, amma sukan jarraba Allah da mugayen ayyukansu su kuwa zauna lafiya.’ ”

16. Sa'an nan mutane waɗanda suke tsoron Ubangiji suka yi magana da junansu, Ubangiji kuwa ya kasa kunne ya ji abin da suke cewa. A gabansa aka rubuta a littafin tarihin waɗanda suke tsoron Ubangiji, suna kuwa girmama shi.

17. “Ni Ubangiji Mai Runduna, na ce, za su zama mutanena na ainihi, a ranar da na aikata. Zan ji ƙansu kamar yadda mahaifi yakan ji ƙan ɗansa wanda suke masa hidima.

18. Sa'an nan za ku ga bambanci tsakanin masu adalci da mugaye, da tsakanin mutumin da yake bauta mini da wanda ba ya bauta mini.”

Karanta cikakken babi Mal 3