Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mal 3:1-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A kan wannan ga abin da Ubangiji Mai Runduna ya amsa, ya ce, “Zan aiki manzona don ya shirya mini hanya, sa'an nan Ubangiji wanda kuke nema zai zo farat ɗaya a cikin Haikalinsa. Manzon da kuke sa zuciyar zuwansa, yana zuwa, zai yi shelar alkawarina.”

2. Amma wa zai iya jurewa da ranar zuwansa? Wa kuma zai tsira sa'ad da ya bayyana? Zai zama kamar wutar da suke bauta ƙarfe, kamar kuma sabulu salo.

3. Zai zo ya yi hukunci kamar wanda yake tace azurfa, ya tsarkake ta. Zai tsarkake firistoci, ya tace su kamar yadda ake yi wa azurfa da zinariya. A sa'an nan ne za su kawo wa Ubangiji hadayun da suka dace.

4. Sa'an nan kuma Ubangiji zai yarda da hadayun mutanen Yahuza da na Urushalima kamar yadda yake a zamanin dā.

5. Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Zan zo wurinku domin in yi shari'a. Nan da nan zan tabbatar da laifin masu yin sihiri, da na mazinata, da na masu shaidar zur, da na masu zaluntar ma'aikata a kan albashinsu, da waɗanda suke ƙwarar gwauraye, wato matan da mazansu suka mutu, da marayu, da baƙi, da waɗanda ba su ganin girmana.”

6. “Ni ne Ubangiji, ba na sākewa, domin haka ku zuriyar Yakubu, ba ku ƙāre ɗungum ba.

7. Ku kamar kakanninku kuke, kun bar bin dokokina, ba ku kiyaye su ba. Ku komo wurina, ni ma zan koma wurinku,” in ji Ubangiji Mai Runduna. “Amma kun ce, ‘Ƙaƙa za mu yi, mu koma gare ka?’

8. Mutum zai iya zambatar Allah? Amma ku kuna zambatata, kuna kuwa cewa, ‘Ta ƙaƙa muka zambace ka?’ A wajen al'amarin zaka da hadayu, kuke zambatata.

9. Dukanku la'antattu ne gama al'ummar duka zamba take yi mini!

10. Ku kawo dukkan zaka a ɗakin ajiyata domin abinci ya samu a cikin Haikalina. Ku gwada ni, za ku gani, zan buɗe taskokin sama in zubo muku da albarka mai yawan gaske.

11. Ba zan bar ƙwari su lalatar da amfanin gonaki ba. Kurangar inabinku za ta cika da 'ya'ya, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.

12. Sa'an nan jama'ar dukan al'ummai za su ce ku masu farin ciki ne, gama ƙasarku za ta yi daɗin zama.”

13. “Kun faɗi mugun abu a kaina,” in ji Ubangiji, “Amma kun ce, ‘Me muka ce a kanka?’

Karanta cikakken babi Mal 3