Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mal 2:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “Yanzu firistoci, ga umarni dominku.

2. Idan ba za ku kasa kunne ba, idan ba za ku sa a zuciyarku ku girmama sunana ba, to, zan aukar muku da la'ana, zan la'antar da albarkunku. Koyanzu ma na riga na la'antar da su domin ba ku riƙe umarnina a zuciyarku ba, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.

3. Ga shi, zan tsauta wa 'ya 'yanku, in watsa kāshin dabbobin hadayunku a fuskokinku, sa'an nan zan kore ku daga gabana.

4. Ta haka za ku sani ni na ba ku wannan umarni domin alkawarin da na yi wa Lawi ya tabbata, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.

5. “Alkawarin da na yi masa na rai ne da salama. Na yi masa alkawaran kuma domin ya ji tsorona, yana kuwa tsorona. Yana kuma tsoron sunana ƙwarai.

6. Koyarwar gaskiya tana cikin bakinsa, ba a sami kuskure a bakinsa ba. Ya yi tafiya tare da ni da salama da gaskiya. Ya kuwa juyo da mutane da yawa daga mugunta.

7. Gama ya kamata bakin firist ya kiyaye ilimi, wajibi ne firistoci su koyar da ilimin gaskiya na Allah, a gare su mutane za su tafi su koyi nufina, domin su manzannina ne, ni Ubangiji Mai Runduna.

8. “Amma ku firistoci kun kauce daga hanya. Kun sa mutane da yawa su karkace saboda koyarwarku. Kun keta alkawarin da na yi da ku, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.

9. Saboda haka, ni ma zan sa jama'ar Isra'ila su raina ku, su ƙasƙantar da ku a gaban dukan mutane, domin ba ku kiyaye umarnina ba, sa'ad da kuke koyar da nufina, kun yi tara.”

10. Ashe, ba dukanmu Ubanmu ɗaya ba ne? Ba Allah nan ɗaya ya halicce mu ba? To, me ya sa muke keta alkawarin da muka yi wa junanmu, muna raina alkawarin da Allah ya yi wa kakanninmu?

11. Mutanen Yahuza sun keta alkawarin da yake tsakaninsu da Allah, sun aikata mugun abu a Isra'ila, da a Urushalima. Gama sun ƙazantar da Haikalin da Ubangiji yake ƙauna, sun kuma auro matan da suke bauta wa gumaka.

Karanta cikakken babi Mal 2