Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mal 1:6-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Ubangiji Mai Runduna ya ce wa firistoci, “Ɗa yakan girmama mahaifinsa, bara kuwa yakan girmama maigidansa. Ni Ubanku ne, me ya sa ba ku girmama ni ba? Ni kuma Maigidanku ne, me ya sa ba ku ganin darajata? Kun raina ni, duk da haka kuna tambaya cewa, ‘Ƙaƙa muka raina ka?’

7. Yadda kuka yi ke nan. Kun miƙa haramtacciyar hadaya ta abinci a kan bagadena, sa'an nan kuna cewa, ‘Ta ƙaƙa muka raina ka?’ To, zan faɗa muku, don kun ƙazantar da bagadena.

8. Sa'ad da kuka kawo makauniyar dabba don ku miƙa mini hadaya, kuna tsammani wannan daidai ne? Ko kuwa sa'ad da kuka kawo gurguwar dabba ko marar lafiya wannan daidai ne? Ku ba mai mulkinku irin wannan ku gani. Zai yi murna? Ko za ku sami tagomashi, a wurinsa? Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.”

9. To, firistoci ku gwada, ku roƙi Allah domin ya yi mana alheri. Ai, ba zai amsa addu'arku ba, wannan kuwa laifinku ne. Ubangiji Mai Runduna ya faɗa.

10. “Da ma wani daga cikinku ya rufe ƙofofin Haikali don kada ku shiga, ku hura wuta marar amfani a bisa bagadena! Ban ji daɗinku ba. Ba zan karɓi hadayun da kuke kawo mini ba,” in ji Ubangiji Mai Runduna.

11. “Mutane daga kowaɗanne sassa na duniya za su girmama ni. Ko'ina za su ƙona mini halattacciyar hadaya, gama dukansu za su girmama ni,” in ji Ubangiji Mai Runduna.

12. “Amma ku kun raina ni da yake kuka ce bagadena ba kome ba ne, kuna raina abincin da kuke ajiyewa a kai.

13. Kuka kuma ce, ‘Mun gaji da wannan irin abu fa!’ Kuna hura mini hanci. Kukan kawo satacciyar dabba, ko gurguwa ko marar lafiya, ku yi mini hadaya da ita! Kuna tsammani zan karɓi wannan daga gare ku?

14. La'ananne ne macucin da yake da lafiyayyun dabbobi da ya alkawarta zai ba ni daga cikin garkensa ya kuwa miƙa mini hadaya ta haramtacciyar dabba. Gama ni babban Sarki ne, dukan al'ummai kuwa suna jin tsoron sunana, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.”

Karanta cikakken babi Mal 1