Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mak 5:14-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Tsofaffi sun daina zama a dandalin ƙofar birni,Samari kuma sun daina bushe-bushe.

15. Farin cikinmu ya ƙare,Raye-rayenmu sun zama makoki.

16. Rawani ya fāɗi daga kanmu,Tamu tu ƙare, gama mun yi zunubi!

17. Saboda wannan zuciyarmu ta ɓaci,Idanunmu kuma suka duhunta.

18. Gama Dutsen Sihiyona ya zama kufai,Wurin yawon diloli.

19. Amma ya Ubangiji, kai ne kake mulki har abada,Kursiyinka ya dawwama har dukan zamanai.

20. Don me ka manta da mu har abada?Don me ka yashe mu da daɗewa haka?

Karanta cikakken babi Mak 5