Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mak 5:12-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. An rataye shugabanni da hannuwansu,Ba a kuma girmama dattawa ba.

13. An tilasta wa samari su yi niƙa,Yara kuma suna tagataga da kayan itace.

14. Tsofaffi sun daina zama a dandalin ƙofar birni,Samari kuma sun daina bushe-bushe.

15. Farin cikinmu ya ƙare,Raye-rayenmu sun zama makoki.

16. Rawani ya fāɗi daga kanmu,Tamu tu ƙare, gama mun yi zunubi!

17. Saboda wannan zuciyarmu ta ɓaci,Idanunmu kuma suka duhunta.

18. Gama Dutsen Sihiyona ya zama kufai,Wurin yawon diloli.

19. Amma ya Ubangiji, kai ne kake mulki har abada,Kursiyinka ya dawwama har dukan zamanai.

20. Don me ka manta da mu har abada?Don me ka yashe mu da daɗewa haka?

21. Ya Ubangiji, ka komo da mu zuwa gare ka!Mu kuwa za mu koma.Ka sabunta kwanakinmu su zama kamar na dā.

Karanta cikakken babi Mak 5