Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mak 3:43-48 Littafi Mai Tsarki (HAU)

43. “Ka yafa fushi, ka runtume mu,Kana karkashe mu ba tausayi.

44. Ka kuma rufe kanka da gajimareDon kada addu'a ta kai wurinka.

45. Ka maishe mu shara da juji a cikin mutane.

46. “Dukan maÆ™iyanmu suna yi mana ba'a.

47. Tsoro, da wushefe,Da lalatarwa, da hallakarwa sun auka mana.

48. Hawaye suna gangarawa daga idanuna kamar ruwan koguna,Saboda an hallaka mutanena.

Karanta cikakken babi Mak 3