Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mak 3:17-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. An raba ni da salama,Na manta da abar da ake ce da ita wadata.

18. Sai na ce, “Darajata ta ƙare,Ba ni kuma da sa zuciya wurin Ubangiji.”

19. Ka tuna da azabata, da galabaitata,Da ɗacin raina, da kumallon da nake fama da shi.

20. Kullum raina yana tunanin azabaina,Raina kuwa ya karai.

21. Da na tuna da wannan, sai na sa zuciya ga gaba.

22. Ƙaunar Ubangiji ba ta ƙarewa,Haka kuma jiyejiyanƙansa ba su ƙarewa.

23. Su sababbi ne kowace safiya,Amincinka kuma mai girma ne.

24. Na ce, “Ubangiji shi ne nawa,Saboda haka zan sa zuciya gare shi.”

25. Ubangiji mai alheri ne ga waɗanda suke sauraronsa,Da wanda suke nemansa kuma.

26. Yana da kyau a jira ceton Ubangiji da natsuwa,

27. Yana da kyau mutum ya hori kansa tun yana yaro.

28. Bari ya zauna a kaɗaice, ya yi shiruSa'ad da yake da damuwa.

29. Bari ya kwanta cikin ƙura,Watakila akwai sauran sa zuciya.

Karanta cikakken babi Mak 3