Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 7:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “Sa'ad da Ubangiji Allahnku ya kai ku ƙasar da kuke shiga ku mallake ta, zai korar muku da al'ummai da yawa, su Hittiyawa, da Girgashiyawa, da Amoriyawa, da Kan'aniyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa, al'umma bakwai ke nan, waɗanda suka fi ku yawa, da kuma ƙarfi.

2. Sa'ad da Ubangiji Allahnku ya bashe su a hannunku, kuka kuma ci nasara a kansu, sai ku hallaka su sarai. Kada ku yi alkawari da su, kada kuma ku yi musu jinƙai.

3. Kada ku yi aurayya da su. Kada ku aurar wa ɗansu da 'yarku, kada kuma ku auro wa ɗanku 'yarsu.

4. Gama za su sa 'ya'yanku su bar bina, su bauta wa gumaka. Wannan zai sa Ubangiji ya husata, ya hallaka ku da sauri.

Karanta cikakken babi M. Sh 7