Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 33:26-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

26. “Babu wani kamar Allahn Yeshurun,Wanda yakan sauko daga Sama don ya cece ka,Wanda ya sauko daga bisa da ɗaukakarsa.

27. Allah Madawwami, shi ne wurin zamanka,Madawwaman damatsansa suna tallafarka,Yana kore maka maƙiyanka,Ya ce, ‘Ka hallaka su!’

28. Da haka Isra'ila yana zaune lafiya,Zuriyar Yakubu tana zaune ita kaɗaiA ƙasa mai hatsi da ruwan inabi,Wurin da raɓa take zubowa daga sama.

29. Mai farin ciki ne kai, ya Isra'ila!Wane ne kamarku, mutanen da Ubangiji ya ceta?Ubangiji ne garkuwarku,Shi ne kuma takobinku mai daraja.Magabtanku za su yi muku fādanci,Amma ku za ku tattake masujadansu.”

Karanta cikakken babi M. Sh 33