Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 32:25-39 Littafi Mai Tsarki (HAU)

25. Waɗanda suke a waje, takobi zai kashe su,A cikin ɗakuna kuma tsoro,Zai hallaka saurayi da budurwa,Da mai shan mama da mai furfura.

26. Na ce, “Zan watsar da su,In sa a manta da su cikin mutane.”

27. Amma saboda gudun tsokanar maƙiyi,Kada abokan gābansu su zaci su ne suka ci nasara.Ai, ni ne na yi wannan.’

28. “Gama su al'umma ce wadda ba ta yin shawara,Ba su da ganewa.

29. Da suna da hikima, da sun gane wannan,Da za su gane da yadda ƙarshensu zai zama!

30. Ƙaƙa mutum ɗaya zai runtumi dubu,Mutum biyu kuma su kori zambar goma,Sai dai Dutsensu ya sayar da su,Ubangiji kuma ya bashe su?

31. Gama dutsensu ba kamar Dutsenmu ba ne,Ko abokan gabanmu ma sun san haka.

32. Kurangar inabinsu daga kurangar inabin Saduma neDa gonakin Gwamrata.'Ya'yan inabinsu dafi ne,Nonnansu masu ɗaci ne.

33. Ruwan inabinsu dafin macizai ne.Da mugun dafin kumurci.

34. “ ‘Wannan ba a jibge suke a rumbunana ba,A ƙulle kuma a taskokina?

35. Sakayya da ɗaukar fansa nawa ne,A lokacin ƙafarsu za ta zame,Gama ranar masifarsu ta kusa,Hallakarsu za ta zo da sauri.’

36. Ubangiji zai ɗauka wa jama'arsa fansa,Zai ji ƙan bayinsa,Sa'ad da ya ga ƙarfinsu ya kāsa,Ba kuma wanda ya ragu, bawa ko ɗa.

37. Sa'an nan zai ce, ‘Ina gumakansu,Dutse wanda suka nemi mafaka gare shi,

38. Waɗanda suka ci kitsen hadayunsu,Suka sha ruwan inabin hadayarsu ta sha?Bari su tashi su taimake ku,Bari su zama mafaka!

39. “ ‘Ku duba fa, ni ne shi,Ba wani Allah, banda ni,Nakan kashe, in rayar,Nakan sa rauni, nakan kuma warkar,Ba wanda zai cece su daga hannuna.

Karanta cikakken babi M. Sh 32