Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 3:6-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Muka hallaka su ƙaƙaf kamar yadda muka yi da Sihon, Sarkin Heshbon. Muka hallaka kowane gari, da mata da maza, da yara.

7. Amma muka riƙe dabbobi da dukiyar da muka kwaso daga garuruwan, ganima.

8. “A lokacin ne fa muka ƙwace wannan ƙasa daga hannun sarakunan nan biyu na Amoriyawa, wato ƙasa wadda take a hayin Urdun, daga kwarin kogin Arnon zuwa Dutsen Harmon.”

9. (Sidoniyawa suka kira Harmon, Siriyon, amma Amoriyawa suna ce da shi Senir.)

Karanta cikakken babi M. Sh 3