Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 3:27-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

27. Ka hau kan ƙwanƙolin Dutsen Fisga, ka dubi gabas, da yamma, da kudu, da arewa. Ka dubi ƙasar da idanunka, gama ba za ka haye Urdun ba.

28. Amma ka umarci Joshuwa, ka ƙarfafa shi. Shi ne zai jagorar jama'ar nan, su haye, shi ne kuma wanda zai rarraba musu gādon ƙasar da za ka gani.’

29. “Sai muka zauna a kwari daura da Bet-feyor.”

Karanta cikakken babi M. Sh 3