Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 22:19-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. su ci shi tara shekel ɗari na azurfa, su ba mahaifin yarinyar, gama a fili mutumin ya ɓata sunan budurwar cikin Isra'ila. Za ta zama matarsa, ba shi da iko ya sake ta muddin ransa.

20. “Idan aka tabbatar zargin gaskiya ne, ba a kuma ga shaidar budurcinta ba,

21. sai a kai yarinyar a ƙofar gidan mahaifinta, sa'an nan mutanen garin su jajjefe ta da duwatsu har ta mutu, don ta yi aikin wauta cikin Isra'ila, gama ta yi karuwanci a gidan mahaifinta. Ta haka za ku kawar da mugunta daga cikinku.

22. “Idan aka iske wani yana kwance da matar wani, sai a kashe dukansu biyu, wato mutumin da matar. Haka za ku kawar da mugunta daga Isra'ila.

23. “Idan a cikin gari wani ya iske budurwar da ake tashinta, ya kwana da ita,

24. sai a kawo su, su biyu ɗin, a dandalin ƙofar gari, ku jajjefe su da duwatsu har su mutu, don yarinyar tana cikin gari, amma ba ta yi kururuwa a taimake ta ba, don kuma mutumin ya ɓata budurwar maƙwabcinsa. Da haka za ku kawar da mugunta daga cikinku.

25. “Amma idan a saura wani ya fāɗa wa yarinyar da ake tashinta, har ya kwana da ita ƙarfi da yaji, sai a kashe wannan mutum.

26. Amma ita yarinyar ba za a yi mata kome ba, domin ba ta yi laifin da ya isa mutuwa ba, gama wannan shari'a daidai take da ta mutumin da ya faɗa wa maƙwabcinsa ya kashe shi.

27. Gama sa'ad da ya same ta a saura, ita wadda ake tashinta ta yi kururuwa, amma ba wanda zai cece ta.

28. “Idan wani ya iske yarinyar da ba a tashinta, ya kama ta, ya kwana da ita, aka kuwa same su,

29. to, sai wanda ya kwana da ita ya ba mahaifinta shekel hamsin na azurfa, ita kuwa za ta zama matarsa, gama ya ci mutuncinta. Ba zai sake ta ba muddin ransa.

Karanta cikakken babi M. Sh 22