Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 21:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “Idan aka iske gawar mutum wanda wani ya kashe a fili a ƙasar da Ubangiji Allahnku ya ba ku, ku mallaka, ba a kuwa san wanda ya kashe shi ba,

2. sai dattawanku da alƙalanku su fito su auna nisan wurin daga gawar zuwa garuruwan da yake kewaye da gawar.

3. Dattawan garin da ya fi kusa da gawar za su ɗauki karsana wadda ba a taɓa aiki da ita ba, ba a kuma taɓa sa mata karkiya ba.

4. Sai dattawan garin nan su kai karsanar kwari inda ruwa yake gudu, inda ba a taɓa noma ko shuka ba. A can cikin kwarin za a karya wuyan karsanar.

5. Sa'an nan sai firistoci, 'ya'yan Lawiyawa, su fito gaba, gama su ne Ubangiji Allahnku ya zaɓa don su yi masa aiki, su sa albarka da sunansa, su ne kuma masu daidaita kowace gardama da cin mutunci.

6. Sai dukan dattawan garin da ya fi kusa da gawar su wanke hannuwansu a bisa karsanar da aka karya wuyanta a kwarin.

Karanta cikakken babi M. Sh 21