Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24
  25. 25
  26. 26
  27. 27
  28. 28
  29. 29
  30. 30
  31. 31
  32. 32
  33. 33
  34. 34

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Biranen Mafaka, Iyakoki na Dā

1. “Sa'ad da Ubangiji Allahnku ya hallaka al'ummai waɗanda zai ba ku ƙasarsu, sa'ad da kuka kore su, kuka zauna cikin garuruwansu da gidajensu,

2. sai ku keɓe garuruwa uku a ƙasar da Ubangiji Allahnku ya ba ku, ku mallaka.

3. Sai ku shirya hanyoyi, ku kuma raba yankin ƙasa wanda Ubangiji Allahnku zai ba ku ku mallaka kashi uku, domin wanda ya yi kisankai ya gudu zuwa can.

4. Wannan shi ne tanadi domin wanda ya yi kisankai, wato wanda zai gudu zuwa can don ya tsira. Idan ya kashe abokinsa ba da niyya ba, ba kuma ƙiyayya a tsakaninsu a dā,

5. misali, idan mutum ya tafi jeji, shi da abokinsa don su saro itace. Da ya ɗaga gatari don ya sari itace, sai ruwan gatarin ya kwaɓe daga ƙotar, ya sari abokinsa har ya mutu. Irin wannan mai kisankai zai gudu zuwa ɗaya daga cikin biranen don ya tsira,

6. don kada mai bin hakkin jini ya bi shi da zafin fushinsa, ya cim masa, saboda nisan hanyar, har ya kashe shi, ko da yake bai cancanci mutuwa ba, tun da ya ke ba ƙiyayya tsakaninsa da abokinsa a dā.

7. Domin haka na umarce ku, ku keɓe wa kanku garuruwa uku.

8. “Sa'ad da Ubangiji Allahnku ya fāɗaɗa ƙasarku kamar yadda ya alkawarta wa kakanninku, har ya ba ku dukan ƙasar da ya alkawarta zai ba kakanninku,

9. in dai kun lura, kun kiyaye umarnin da nake umartarku da shi yau, ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya cikin tafarkunsa kullum, sa'an nan sai ku ƙara garuruwa uku a kan waɗannan uku ɗin kuma,

10. don kada a zubar da jinin marar laifi a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku gādo, domin kada alhakin jini ya kama ku.

11. “Amma idan wani mutum yana ƙin wani ya kuwa tafi ya yi fakonsa, ya tasar masa, ya yi masa rauni har ya mutu, sa'an nan ya gudu zuwa ɗaya daga cikin garuruwan nan,

12. sai dattawan garinsu su aiko, a kamo shi daga can, sa'an nan su bashe shi ga mai bin hakkin jini don a kashe shi.

13. Kada ku ji tausayinsa. Ta haka za ku hana zub da jinin marar laifi cikin Isra'ila, don ku sami zaman lafiya.

14. “A cikin gādon da za ku samu a ƙasar da Ubangiji Allah yake ba ku ku mallaka, kada ku ci iyakar maƙwabcinku, wanda kakan kakanni suka riga suka kafa.”

Doka a kan Ba da Shaida

15. “Shaidar mutum ɗaya ba za ta isa a tabbatar, cewa mutum ya yi laifi ba, sai a ji shaidar mutum biyu ko uku, kafin a tabbatar da laifin mutum.

16. Idan ɗan sharri ya ba da shaidar zur a kan wani,

17. sai su biyu ɗin su zo a gaban Ubangiji, su tsaya a gaban firistoci da alƙalai waɗanda suke aiki a lokacin.

18. Sai alƙalan su yi bincike sosai. Idan ɗan sharrin ya ba da shaidar zur a kan ɗaya mutumin,

19. to, sai ku yi masa kamar yadda ya so a yi wa wancan mutumin. Ta haka za ku kawar da mugunta daga cikinku.

20. Sauranku za su ji, su ji tsoro, ba za a ƙara aikata irin wannan mugunta ba.

21. Kada ku ji tausayi, zai zama rai maimakon rai, ido maimakon ido, haƙori maimakon haƙori, hannu maimakon hannu, ƙafa maimakon ƙafa.”