Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 10:9-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Domin haka kabilar Lawi ba su da rabo ko gādo tare da 'yan'uwansu, Ubangiji shi ne gādonsu kamar yadda Ubangiji Allahnku ya faɗa musu.)

10. “Na sāke yin dare arba'in da yini arba'in a kan dutsen kamar dā. Ubangiji kuwa ya amsa addu'ata a lokacin kuma, ya janye hallaka ku.

11. Sai Ubangiji ya ce mini, ‘Tashi, ka tafi, ka kama tafiyarka a gaban jama'an nan domin su je, su shiga, su mallaki ƙasar da na rantse wa kakanninsu, zan ba su.’ ”

12. “Yanzu fa, ya Isra'ilawa ga abin da Ubangiji Allahnku yake so a gare ku. Sai ku ji tsoron Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya cikin hanyoyinsa, ku ƙaunace shi, ku bauta wa Ubangiji Allahnku da zuciya ɗaya da dukan ranku.

13. Ku kiyaye umarnan Ubangiji da dokokinsa waɗanda nake umurtarku da su yau don amfanin kanku.

14. Duba, saman sammai, da duniya, da dukan abin da yake cikinta na Ubangiji Allahnku ne.

15. Duk da haka Ubangiji ya ƙaunaci kakanninku ya zaɓi zuriyarsu a bayansu daga cikin dukan sauran al'umma, kamar yadda yake a yau.

16. Saboda haka sai ku kame zukatanku, kada ku ƙara yin taurinkai.

17. Gama Ubangiji Allahnku, Allahn alloli ne, da Ubangijin iyayengiji. Shi Allah mai girma ne, mai iko, mai bantsoro, wanda ba ya son zuciya, ba ya karɓar hanci.

18. Yakan yi wa marayu da gwauraye na gaske shari'a da adalci. Yana ƙaunar baƙo, yakan ba shi abinci da sutura.

19. Sai ku ƙaunaci baƙo, gama dā ku baƙi ne a ƙasar Masar.

20. Sai kuma ku ji tsoron Ubangiji Allahnku, ku bauta masa. Ku manne masa, ku yi rantsuwa da sunansa.

21. Shi ne abin yabonku, shi ne Allahnku, wanda ya yi muku waɗannan al'amura masu girma, masu bantsoro waɗanda kuka gani da idanunku.

22. Kakanninku saba'in ne suka gangara zuwa Masar, amma yanzu Ubangiji Allahnku ya riɓaɓɓanya ku, kuka yi yawa kamar taurarin sama.”

Karanta cikakken babi M. Sh 10