Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 10:12-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. “Yanzu fa, ya Isra'ilawa ga abin da Ubangiji Allahnku yake so a gare ku. Sai ku ji tsoron Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya cikin hanyoyinsa, ku ƙaunace shi, ku bauta wa Ubangiji Allahnku da zuciya ɗaya da dukan ranku.

13. Ku kiyaye umarnan Ubangiji da dokokinsa waɗanda nake umurtarku da su yau don amfanin kanku.

14. Duba, saman sammai, da duniya, da dukan abin da yake cikinta na Ubangiji Allahnku ne.

15. Duk da haka Ubangiji ya ƙaunaci kakanninku ya zaɓi zuriyarsu a bayansu daga cikin dukan sauran al'umma, kamar yadda yake a yau.

16. Saboda haka sai ku kame zukatanku, kada ku ƙara yin taurinkai.

17. Gama Ubangiji Allahnku, Allahn alloli ne, da Ubangijin iyayengiji. Shi Allah mai girma ne, mai iko, mai bantsoro, wanda ba ya son zuciya, ba ya karɓar hanci.

18. Yakan yi wa marayu da gwauraye na gaske shari'a da adalci. Yana ƙaunar baƙo, yakan ba shi abinci da sutura.

19. Sai ku ƙaunaci baƙo, gama dā ku baƙi ne a ƙasar Masar.

20. Sai kuma ku ji tsoron Ubangiji Allahnku, ku bauta masa. Ku manne masa, ku yi rantsuwa da sunansa.

21. Shi ne abin yabonku, shi ne Allahnku, wanda ya yi muku waɗannan al'amura masu girma, masu bantsoro waɗanda kuka gani da idanunku.

Karanta cikakken babi M. Sh 10