Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 1:43-46 Littafi Mai Tsarki (HAU)

43. Haka kuwa na faɗa muku, amma ba ku kasa kunne ba, kuka ƙi yin biyayya da umarnin Ubangiji. Sai kuka yi izgili, kuka hau cikin ƙasar tuddai.

44. Sai Amoriyawa waɗanda suke zaune a ƙasar tuddai suka fito da yawa kamar ƙudan zuma, suka taru a kanku suka bi ku, suka fatattaka ku a Seyir, har zuwa Horma.

45. Sai kuka koma, kuka yi kuka ga Ubangiji, amma Ubangiji bai ji kukanku ba, bai kuma kula da ku ba.

46. Kun kuwa zauna cikin Kadesh kwana da kwanaki, kamar dai yadda kuka yi.”

Karanta cikakken babi M. Sh 1