Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 1:23-32 Littafi Mai Tsarki (HAU)

23. “Na ga al'amarin ya gamshe ni, saboda haka na ɗauki mutum goma sha biyu daga cikinku, mutum guda daga kowace kabila.

24. Mutanen kuwa suka kama hanya, suka tafi tuddai, suka kuma isa kwarin Eshkol, suka leƙo asirin ƙasar.

25. Da hannunsu suka ɗebo daga cikin amfanin ƙasar, suka gangaro mana da shi. Suka kuma faɗa mana cewa ƙasa wadda Ubangiji Allahnmu yake ba mu, mai kyau ce.

26. “Amma kuka ƙi ku haura, kuka ƙi bin umarnin Ubangiji Allahnku.

27. Sai kuka yi ta gunaguni cikin alfarwanku, kuna cewa, ‘Ai, saboda Ubangiji ya ƙi mu, shi ya sa ya fisshe mu daga ƙasar Masar, don ya bashe mu a hannun Amoriyawa, su hallaka mu.

28. Ta ƙaƙa za mu hau? Gama 'yan'uwanmu sun narkar da zuciyarmu da cewa, mutanen sun fi mu girma, sun kuma fi mu ƙarfi. Biranensu kuma manya manya ne, da gine-gine masu tsayi ƙwarai. Har ma sun ga Anakawa a wurin.’

29. “Sai na ce muku, ‘Kada ku ji tsoronsu ko ku firgita.

30. Ubangiji Allahnku wanda yake tafiya tare da ku, shi kansa zai yi yaƙi dominku kamar yadda ya yi muku a Masar a kan idonku.

31. Kun ma ga yadda Ubangiji ya bi da ku cikin jeji kamar yadda mutum yakan bi da ɗansa, a dukan tafiyarku har zuwa wannan wuri.’

32. Amma ko da yake ya yi muku haka duk da haka ba ku dogara ga Ubangiji Allahnku ba.

Karanta cikakken babi M. Sh 1