Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Had 6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Rashin Ma'anar Rai

1. Na kuma lura, a duniyan nan an yi wa ɗan adam rashin adalci ƙwarai.

2. Allah yakan ba wani mutum dukiya, da daraja, da wadata, i, da kowane abu da yake bukata. Amma bai ba shi iko ya more su ba. A maimakonsa wani baƙo ne zai more su. Wannan aikin banza ne ba kuwa daidai ba ne.

3. Mai yiwuwa ne mutum ya haifi 'ya'ya ɗari ya kuma yi tsawon rai, amma kome tsawon ransa ba wani abu ba ne idan ba shi da farin ciki, bai kuma sami kyakkyawar binnewa ba. Sai na ce, gara jaririn da aka haifa matacce da shi.

4. Haihuwar ba ta amfane shi kome ba, gama ya zo daga duhu ya koma duhu inda aka manta da shi.

5-6. Gama bai taɓa ganin hasken rana ba, bai kuma san abin da ake ce da shi rai ba. Amma duk da haka ya dai huta, fiye da mutumin da bai more wa rai ba, ko da ya shekara dubu biyu. Duk da haka dukansu wuri ɗaya za su tafi.

7. Dukan wahalar da ɗan adam yake yi ta samun abinci ce, amma duk da haka bai taɓa ƙoshi ba.

8. Da me mai hikima ya fi wawa? Wace riba ce kuma matalaucin da ya iya zama da mutane zai samu?

9. Abin da ya zo hannu ya fi dogon buri gama dogon buri aikin banza ne, harbin iska kawai.

10. Kowane abu da ya kasance, an riga an ba shi suna, yadda aka yi mutum haka zai zama. Ba kuwa zai iya gardama da abin da ya fi ƙarfinsa ba.

11. Yawan magana yakan ɓata al'amari. Wane amfani zai yi wa mutum?

12. Wa ya san abin da ya fi dacewa ga mutum a 'yan kwanakinsa marasa amfani? Sukan wuce kamar inuwa. Wa kuma zai iya faɗa wa mutum abin da zai faru a duniya bayan rasuwarsa?