Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Had 5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Kada ka Yi Gaggawar Yin Wa'adi

1. Ka yi hankali lokacin da kake shiga Haikali. Gara ka tafi can da niyyar koyon wani abu, da ka miƙa hadaya kamar waɗansu wawaye da ba su san halal da haram ba.

2. Yi tunani kafin ka yi magana, kada ka yi wa Allah wa'adi na gaggawa. Allah yana Sama kai kuwa kana duniya. Don haka kada ka faɗa fiye da abin da ya kamata.

3. Yawan damuwarka yana iya sa ka yi mafarkai. Yawan maganarka kuma yana iya sa ka ka yi maganar wauta.

4. Sa'ad da ka yi wa'adi ga Allah, yi hanzari ka cika, gama wawa ba shi da wani amfani a gare shi. Sai ka cika wa'adin da ka yi!

5. Gara kada ka yi wa'adi, da ka yi wa'adi, amma ba ka cika ba.

6. Kada ka bar maganar bakinka ta kai ka ga yin zunubi, har ka ce wa manzon Allah, ba haka kake nufi ba. Don me za ka sa Allah ya yi fushi da kai, har ya hallakar da abin da ka yi wahalarsa?

7. Yawan mafarkanka, da dukan ayyukanka, da yawan maganganunka duk banza ne, duk da haka ya fi maka amfani ka yi tsoron Allah.

Rai Banza Ne

8. Idan ka ga hukuma na zaluntar talakawa, ba ta yi musu adalci, ba ta kiyaye hakkinsu, kada ka yi mamaki. Kowane shugaba yana da shugaban da yake goyon bayansa. Dukansu biyu suna da goyon bayan manyan shugabanni.

9. Abin da ƙasa take bukata, shi ne sarkin da yake kulawa da aikin gona.

10. Idan kana ƙaunar kuɗi, daɗi ba zai ishe ka ba, wanda kuma yake ƙaunar dukiya, ba zai ƙoshi da riba ba, wannan kuma aikin banza ne.

11. Gwargwadon dukiyarka gwargwadon mutanen da za ka ciyar, ribarka kaɗai ita ce sanin kana da dukiya.

12. Ma'aikaci, ko yana da isasshen abinci, ko ba shi da isasshe, duk da haka yakan ji daɗin barcinsa da dare. Amma mawadaci yakan kwana bai rintsa ba, saboda yawan tunani.

13. Wani mugun abu da na gani a duniyan nan, shi ne mutane sun ajiye kuɗi domin lokacin da za su bukace su.

14. Amma sukan lalace saboda muguwar ma'amala, har ba abin da ya ragu da za su bar wa 'ya'yansu gado.

15. Mukan bar duniyan nan kamar yadda muka shigo ta, ba mu da kome. Dukan ayyukanmu, ba abin da za mu ɗauka mu tafi da shi.

16. Wannan mugun abu ne, mukan tafi kamar yadda muka zo. Mukan yi aiki, muna ƙoƙari mu kama iska, me muka samu ke nan?

17. Mun yi zamanmu a duhu, da baƙin ciki, da damuwa, da fushi, da cuta.

18. Ga abin da na gani yana da kyau, ya kuma dace, shi ne kurum mutum ya ci, ya sha, ya ji daɗin aikin da ya yi a 'yan kwanakin rai da Allah ya ba shi, gama wannan shi aka ƙaddara wa mutum.

19. Duk wanda Allah ya ba wadata da dukiya ya kuma bar shi ya ci moriyarsu, sai ya yi godiya ya ci moriyar aikin da ya yi, wannan kyauta ce ta Allah.

20. Tun da yake Allah ya yarje masa, ya zauna da farin ciki, ba ya cika damuwa saboda rashin tsawon kwanaki.