Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Had 3:18-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Na dai ce Allah yana jarraba mutum ne domin ya nuna masa bai ɗara dabba ba.

19. Gama makomar 'yan adam da ta dabbobi ɗaya ce, yadda ɗayan yake mutuwa haka ma ɗayan. Dukansu numfashinsu iri ɗaya ne. Mutum bai fi dabba ba, gama rai ba shi da wata ma'ana ga kowannensu.

20. Dukansu wuri ɗaya za su tafi, gama dukansu biyu daga turɓaya suka fito, dukansu biyu kuma za su koma cikinta.

21. Wa zai iya tabbatarwa, cewa ruhun mutum zai tafi sama, ruhun dabba kuwa zai tafi ƙasa?

22. Na gane abin da ya fi wa mutum, shi ne ya more wahalar aikinsa, gama ba wani abu da zai iya yi. Ba wata hanya da zai san abin da zai faru bayan mutuwarsa.

Karanta cikakken babi M. Had 3