Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Had 2:16-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Gama ba za a ƙara tunawa da mai hikima ko wawa ba, nan gaba za a manta da dukansu. Yadda mai hikima yake mutuwa haka ma wawa yake mutuwa.

17. Saboda haka rai ba wani abu ba ne a gare ni, domin dukan abin da yake cikinsa bai kawo mini kome ba sai wahala. Duka banza ne, ba abin da nake yi sai harbin iska kawai.

18. Daga cikin dukan abin da na samu kan aikin da na yi, ba su da wata ma'ana a gare ni, gama na sani zan bar wa magājina ne.

19. Wa ya sani ko shi mai hikima ne, ko kuma wawa ne? Duk da haka shi zai mallaki dukan abin da na sha wahalar tanadinsa. Dukan aikin da na yi na hikima a wannan duniya aikin banza ne.

20. Na yi baƙin ciki a kan dukan wahalar aikin da na yi a duniya.

21. Kai ne ka yi aiki da dukan hikimarka, da iliminka, da gwanintarka, amma kuma tilas ka bar shi duka ga wanda bai yi wahalar kome a ciki ba. Wannan ma bai amfana kome ba, mugun abu ne.

22. Me mutum zai samu daga cikin aikin da ya yi duka, da irin ɗawainiyar da ya sha a kan yin aikin?

23. Dukan abin da yake yi a kwanakinsa, ba abin da ya jawo masa, sai damuwa da ɓacin zuciya. Da dare ma ba ya iya hutawa. Wannan kuma aikin banza ne duka.

24. Ba abin da ya fi wa mutum kyau fiye da ya ci, ya sha, ya saki jiki, ya ci moriyar aikinsa. Na gane wannan ma daga wurin Allah ne.

25. Ƙaƙa za ka sami abin da za ka ci, ko ka ji daɗin zamanka in ba tare da shi ba?

Karanta cikakken babi M. Had 2