Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Had 1:9-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Abin da ya faru a dā, shi zai sāke faruwa,Abin da aka yi a dā, shi za a sāke yi.A duniya duka ba wani abu da yake sabo.

10. Da akwai wani abu da za a ce,“Duba, wannan sabon abu ne”?Abin yana nan tuntuni kafin zamaninmu.

11. Ba wanda yake iya tunawa da abin da ya faru a dā,Da abin da zai faru nan gaba.Ba wanda zai iya tunawa da abin da zai faruA tsakanin wannan lokaci da wancan.

12. Ni Mai Hadishi sarki ne, na sarauci Isra'ilawa a Urushalima.

13. Na ɗauri aniya in jarraba, in bincika dukan abubuwan da ake yi a duniyan nan.Allah ya ƙaddara mana abu mai wuya.

14. Na ga dukan abin da ake yi a duniya, duk aikin banza ne da ɓata lokaci kawai.

15. Ba za a iya miƙar da abin da ya tanƙware ba, ba kuma za a iya ƙidaya abin da ba shi ba.

16. Na ce wa kaina, “Na zama babban mutum, na fi duk wanda ya taɓa mulkin Urushalima hikima. Hakika na san hikima da ilimi.”

17. Na ɗaura aniya in san bambancin da yake tsakanin ilimi da wauta, da a tsakanin hikima da gāɓanci. Amma na gane harbin iska nake yi kawai.

18. Gwargwadon hikimarka gwargwadon damuwarka, gwargwadon ƙarin iliminka gwargwadon jin haushinka.

Karanta cikakken babi M. Had 1