Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Had 1:4-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Zamani yakan wuce, wani zamani kuma ya zo,Amma abadan duniya tana nan yadda take.

5. Rana takan fito, takan kuma faɗi,Sa'an nan ta gaggauta zuwa wurin fitowarta.

6. Iska takan hura zuwa kudu, ta kuma hura zuwa arewa,Ta yi ta kewayawa, har ta koma inda ta fito.

7. Kowane kogi yakan gangara zuwa teku,Amma har yanzu teku ba ta cika ba.Ruwan yakan koma mafarin kogin,Ya sāke gangarawa kuma.

8. Kowane abu yana sa gajiya,Gajiyar kuwa ta fi gaban magana.Idanunmu ba sā ƙoshi da gani,Haka kuma kunnuwanmu ba sā ƙoshi da ji.

Karanta cikakken babi M. Had 1