Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Had 1:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Maganar Mai Wa'azi ɗan Dawuda, Sarkin Urushalima.

2. Banza a banza ne, in ji Mai Hadishi,Banza a banza ne, dukan kome banza ne.

3. Wace riba ce mutum zai samu daga cikin aikinsa,Da yake yi a duniya?

4. Zamani yakan wuce, wani zamani kuma ya zo,Amma abadan duniya tana nan yadda take.

5. Rana takan fito, takan kuma faɗi,Sa'an nan ta gaggauta zuwa wurin fitowarta.

6. Iska takan hura zuwa kudu, ta kuma hura zuwa arewa,Ta yi ta kewayawa, har ta koma inda ta fito.

7. Kowane kogi yakan gangara zuwa teku,Amma har yanzu teku ba ta cika ba.Ruwan yakan koma mafarin kogin,Ya sāke gangarawa kuma.

Karanta cikakken babi M. Had 1