Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Mah 6:25-35 Littafi Mai Tsarki (HAU)

25. A wannan dare Ubangiji ya ce masa, “Ka ɗauki bijimin mahaifinka, da wani bijimin bana bakwai. Sa'an nan ka rushe bagaden gunkin nan Ba'al na mahaifinka, ka sare gumakan da suke kusa da shi.

26. Sa'an nan ka gina wa Ubangiji Allahnka bagade mai kyau a kan wannan kagara. Ka ɗauki bijimi na biyu ka miƙa shi hadayar ƙonawa da itacen gumakan da za ka sare.”

27. Gidiyon fa ya ɗauki mutum goma daga cikin barorinsa, ya yi yadda Ubangiji ya faɗa masa. Amma domin yana tsoron, mutanen gidansa da na gari, bai yi wannan da rana ba, sai da dare.

28. Da mutanen garin suka tashi da safe, sai ga bagaden Ba'al a farfashe, gumakan kuma da suke kusa da shi, an sare. Bijimi na biyu kuma, an miƙa shi hadaya a kan bagaden da aka gina.

29. Suka ce wa juna, “Wa ya yi wannan abu?” Da suka binbincika, sai suka tarar Gidiyon ne, ɗan Yowash, ya yi shi.

30. Sai suka ce wa Yowash, “Ka kawo ɗanka a kashe, gama ya rushe bagaden gunkin nan Ba'al, ya kuma sare gumakan da suke kusa da shi.”

31. Yowash kuwa ya ce wa dukan waɗanda suka tasar masa, “Za ku yi hamayya domin gunkin nan Ba'al, ko kuwa za ku goyi bayansa? Duk wanda ya yi hamayya dominsa za a kashe shi da safe. Idan shi allah ne, to, bari ya yi hamayya don kansa, gama an farfashe bagadensa.”

32. A ranar nan aka laƙaba wa Gidiyon suna Yerubba'al, wato “Bari gunki Ba'al ya yi hamayya don kansa, domin an farfashe bagadensa.”

33. Dukan Madayanawa kuwa, da Amalekawa, da mutanen gabas suka tattaru. Suka haye, suke kafa sansaninsu a kwarin Yezreyel.

34. Ruhun Ubangiji kuwa ya sauko a kan Gidiyon, sai ya busa ƙaho, mutanen Abiyezer suka bi shi.

35. Ya kuma aiki manzanni a ƙasar Manassa duka. Su kuma aka kirawo su su bi shi. Ya kuma aiki manzanni zuwa ga Ashirawa da Zabalunawa, da Naftaliyawa, su kuma suka zo, suka haɗa kai da shi.

Karanta cikakken babi L. Mah 6