Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Mah 5:20-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Daga sama, taurari suka yi yaƙi,Suna gilmawa a sararin samaSuka yi yaƙi da Sisera.

21. Ambaliyar Kishon ta kwashe su,Wato tsohon Kogin Kishon.Zan yi gaba, in yi gaba da ƙarfi!

22. Sa'an nan dawakai sun yi ta rishiSuna ƙwaƙular ƙasa da kofatansu.

23. Mala'ikan Ubangiji ya ce,“Ka la'anta Meroz,Ka la'anta mazauna cikinta sosai,Gama ba su kawo wa Ubangiji gudunmawa ba,Su zo su yi yaƙi kamar sojoji dominsa.”

24. Wadda ta fi kowa sa'a daga cikin mata, sai Yayel,Matar Eber, Bakene,Wadda ta fi kowa sa'a daga cikin matan da suke a alfarwai.

25. Sisera ya roƙi ruwan sha,Sai ta ba shi madara,Ta kawo masa kindirmo a kyakkyawar ƙwarya.

26. Ta ɗauki turken alfarwa a hannunta,Ta riƙe guduma a guda hannun,Ta bugi Sisera, kansa ya fashe,Ta kwankwatse kansa, ya ragargaje.

27. Ya fāɗi a gwiwoyinta,Ya fāɗi ƙasa, yana kwance shiru a ƙafafunta.A ƙafafunta ya sunkuya ya fāɗi,Ya fāɗi matacce har ƙasa.

28. Mahaifiyar Sisera ta duba ta tagogi,Ta leƙa ta kariyar taga, ta ce,“Me ya sa karusarsa ta yi jinkirin zuwa?Don me dawakansa ba su komo da wuri ba?”

29. 'Yan matanta mafi hikima suka amsa mata,Ita kuwa ta yi nanatawa, tana cewa,

30. “Nema suke kurum su sami ganima, su raba,Yarinya ɗaya ko biyu domin kowane soja,Tufafi masu tsada domin Sisera,Rinannun tufafi masu ado domin sarauniya.”

31. Ta haka, ya Ubangiji ka sa maƙiyanka su mutu,Amma abokanka su haskaka kamar fitowar rana!Ƙasar kuwa ta zauna lafiya shekara arba'in.

Karanta cikakken babi L. Mah 5