Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Mah 5:18-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Amma mutanen Zabaluna da na NaftaliSuka kasai da ransu a bakin dāga.

19. Sarakuna suka zo, suka yi yaƙi a Ta'anak,A rafin Magiddo.Sarakunan Kan'ana suka yi yaƙi,Amma ba su kwashe azurfa ba.

20. Daga sama, taurari suka yi yaƙi,Suna gilmawa a sararin samaSuka yi yaƙi da Sisera.

21. Ambaliyar Kishon ta kwashe su,Wato tsohon Kogin Kishon.Zan yi gaba, in yi gaba da ƙarfi!

22. Sa'an nan dawakai sun yi ta rishiSuna ƙwaƙular ƙasa da kofatansu.

23. Mala'ikan Ubangiji ya ce,“Ka la'anta Meroz,Ka la'anta mazauna cikinta sosai,Gama ba su kawo wa Ubangiji gudunmawa ba,Su zo su yi yaƙi kamar sojoji dominsa.”

24. Wadda ta fi kowa sa'a daga cikin mata, sai Yayel,Matar Eber, Bakene,Wadda ta fi kowa sa'a daga cikin matan da suke a alfarwai.

25. Sisera ya roƙi ruwan sha,Sai ta ba shi madara,Ta kawo masa kindirmo a kyakkyawar ƙwarya.

26. Ta ɗauki turken alfarwa a hannunta,Ta riƙe guduma a guda hannun,Ta bugi Sisera, kansa ya fashe,Ta kwankwatse kansa, ya ragargaje.

27. Ya fāɗi a gwiwoyinta,Ya fāɗi ƙasa, yana kwance shiru a ƙafafunta.A ƙafafunta ya sunkuya ya fāɗi,Ya fāɗi matacce har ƙasa.

Karanta cikakken babi L. Mah 5