Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Mah 5:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A wannan rana Debora da Barak, ɗan Abinowam, suka raira wannan waka,

2. Yabo ya tabbata ga Ubangiji!Isra'ilawa suka ƙudura su yi yaƙi.Mutane suka sa kansu da farin ciki.Alhamdu lillahi!

3. Ku kasa kunnenku ya ku sarakuna,Ku lura, ya ku hakimai,Zan raira waƙa in yi kaɗe-kaɗe ga Ubangiji,Allah na Isra'ila.

4. Ya Ubangiji, sa'ad da ka bar duwatsun Seyir,Sa'ad da ka fito daga jihar Edom,Ƙasa ta girgiza,Ruwan sama ya zubo daga sararin sama,I, gizagizai suka kwararo da ruwa.

5. Duwatsu suka girgiza a gaban Ubangijin Sina'i,A gaban Ubangiji, Allah na Isra'ila.

6. A zamanin Shamgar ɗan Anat, a zamanin Yayel,Ayarori suka daina bi ta ƙasar,Matafiya suka bi ta ƙananan hanyoyi.

7. Garuruwan Isra'ila, ba kowa ciki,Ba kowa ciki, sai da na zo.Na zo kamar uwa ga Isra'ila,

8. Sa'ad da Isra'ilawa suka zaɓi baƙin alloli,Sai ga yaƙi a ƙasar.Ba a ga garkuwa ko mashiA wurin mutum dubu arba'in na Isra'ila ba.

9. Zuciyata tana wajen shugabannin yaƙi na Isra'ila,Da mutanen da suka ba da kansu da farin ciki.Yabo ya tabbata ga Ubangiji!

10. Ku ba da labari,Ku da kuke haye da fararen jakuna,Kuna zaune a shimfiɗu,Ku da dole ku tafi da ƙafa duk inda za ku.

11. Ku kasa kunne! Da hayaniya mutane a bakin rijiyoyiSuna ba da labarin nasarar Ubangiji,Wato nasarar jama'ar Isra'ila!Sa'an nan jama'ar UbangijiSuna tahowa daga biranensu.

12. Ki ja gaba, ke Debora, ki ja gaba!Ki ja gaba! Ki raira waƙa, ki ja gaba!Ka ci gaba, kai Barak,Ɗan Abinowam, ka tasa kamammunka gaba!

Karanta cikakken babi L. Mah 5