Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Mah 19:16-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. To, ga wani tsoho yana komowa daga gona da yamma. Tsohon kuwa mutumin ƙasar tudu ta Ifraimu ne, yana zama a Gibeya, amma mutanen Gibeya kabilar Biliyaminu ne.

17. Da dattijon ya duba ya ga matafiyin a dandalin birnin, ya ce masa, “Ina za ka? Daga ina kuma ka fito?”

18. Balawen ya ce masa, “Muna tahowa ne daga Baitalami ta Yahudiya zuwa wani lungun da take ƙasar tudu ta Ifraimu, inda nake. Na je Baitalami ta Yahudiya ne, yanzu kuwa ina komawa gida. Ba wanda ya sauke ni a gidansa.

19. Ina da baro domin jakuna, ina kuma da abinci da ruwa inabi don kaina, da ƙwarƙwarata da barana, ba mu rasa kome ba.”

20. Tsohon nan ya ce, “Ku zo mu je gidana, duk abin da kuke bukata zan ba ku, amma kada ku kwana a dandalin.”

21. Sai ya kai su gidansa, ya ba jakan harawa, aka wanke ƙafafun baƙin, sa'an nan suka ci suka sha.

22. Sa'ad da suke cikin jin daɗin ci da sha, 'yan iskan da suke birnin suka zo suka kewaye gidan, suka yi ta bubbuga ƙofar, suka ce wa tsohon, “Ka fito mana da mutumin da ya zo gidanka don mu yi luɗu!”

23. Tsohon kuwa ya fito wurinsu, ya ce musu, “A'a, 'yan'uwana, kada ku yi mugun abu haka, wannan ya sauka a gidana, kada ku yi wannan rashin kunya.

24. Ga 'yata budurwa da ƙwarƙwararsa, bari in fito muku da su, ku yi abin da kuka ga dama da su, amma kada ku yi wa mutumin nan wannan abin kunya!”

25. Amma 'yan iskan ba su yarda ba, sai Balawen ya fitar da ƙwarƙwararsa gare su. Suka yi mata faɗe, suka wulakanta ta dukan dare har kusan wayewar gari, sa'an nan suka ƙyale ta.

26. Da gari ya waye, ƙwarƙwarar ta zo ta fāɗi a ƙofar gidan tsohon, inda maigidanta ya sauka, tana nan har hantsi ya cira.

27. Sa'ad da Balawen ya tashi da safe, ya buɗe ƙofa, ya fita domin ya kama hanyarsa, sai ga ƙwarƙwararsa kwance a ƙofar gida, da hannuwanta a dokin ƙofar.

28. Ya ce mata, “Tashi mu tafi.” Amma ba amsa. Sai ya aza gawarta a kan jaki, sa'an nan ya kama hanya zuwa gida.

29. Da ya isa gida, ya ɗauki wuƙa ya yanyanka gawar ƙwarƙwararsa gunduwa gunduwa har goma sha biyu, ya aika a ko'ina cikin dukan ƙasar Isra'ila.

Karanta cikakken babi L. Mah 19