Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Mah 18:18-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Sa'ad da mutum biyar ɗin nan suka shiga gidan Mika suka ɗauki falmaran, da sassaƙaƙƙen gunki, da kan gida, da gunki na zubi, sai firist ɗin ya ce musu, “Me kuke yi?”

19. Suka ce masa, “Yi mana shiru, kame bakinka. Ka biyo mu, ka zama firist namu da mai ba mu shawara. Bai fi kyau ka zama firist na kabilar Isra'ila ba, da a ce ka zama na gidan mutum guda kawai?”

20. Da firist ɗin ya ji haka, sai ya yi murna, ya ɗauki falmaran da kan gida da sassaƙaƙƙen gunki, ya tafi tare da su.

21. Suka juya, suka tafi da 'ya'yansu da dabbobinsu, da mallakarsu.

22. Sa'ad da suka yi 'yar tazara daga gidan Mika sai aka kira maƙwabtan Mika, suka je suka ci wa Danawa.

23. Suka yi wa Danawa tsawa. Da suka waiga, sai suka ce wa Mika, “Me ya faru? Me ya kawo waɗannan 'yan iska?”

24. Mika kuwa ya ce musu, “Kun kwashe allolina da na yi, da firist ɗina, me ya rage mini kuma? Sa'an nan ku ce mini, ‘Me ya faru?’ ”

25. Danawa kuma suka ce masa, “Kada ka kuskura ka ce kome, idan ba haka ba mutanen nan za su harzuƙa, da kai da iyalinka duka ku rasa rayukanku.”

26. Sa'an nan Danawa suka kama hanyarsu. Da Mika ya ga dai sun fi ƙarfinsa, sai ya juya ya koma gida.

27. Da Danawa suka ɗauke gumakan da Mika ya yi, da firist ɗinsa, sai suka je Layish inda suka sami mutane suna zamansu a huce. Suka hallaka su, suka ƙone birnin.

28. Ba wanda zai ceci mutanen Layish, gama suna nesa da Sidon, ba su kuma sha'ani da kowa. A kwari guda ne da Bet-rehob. Danawa kuwa suka sāke gina birnin, suka zauna a ciki.

29. Suka sa wa birnin suna Dan, ɗan Yakubu. Kafin wannan lokaci kuwa ana kiran birnin Layish ne.

Karanta cikakken babi L. Mah 18