Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Mah 17:6-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. A wannan lokaci ba sarki a Isra'ila, kowa yana ta yin yadda ya ga dama.

7. Akwai wani saurayi Balawen da yake zama a Baitalami ta Yahudiya.

8. Saurayin kuwa ya yi ƙaura daga Baitalami. Sa'ad da yake tafiya sai ya iso gidan Mika, a ƙasar tudu ta Ifraimu.

9. Mika ya tambaye shi, “Daga ina ka zo?”Ya ce, “Ni Balawe ne na Baitalami ta Yahudiya, ina neman wurin da zan zauna.”

10. Mika ya ce masa, “Ka zauna tare da ni, ka zama mai ba ni shawara, da kuma firist, ni kuwa zan riƙa ba ka azurfa goma, da tufafi, da abin zaman gari kowace shekara.”

11. Balawen kuwa ya yarda ya zauna tare da Mika. Ya kuwa zama kamar ɗa ga Mika.

12. Mika kuma ya naɗa shi ya zama firist ɗinsa. Ya kuwa zauna a gidansa.

Karanta cikakken babi L. Mah 17