Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Mah 15:9-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Filistiyawa suka haura, suka kafa sansani a Yahudiya, suka bazu a cikin Lihai.

10. Mutanen Yahuza suka ce, “Me ya sa kuka kawo mana yaƙi?”Filistiyawa suka ce, “Mun zo ne domin mu kama Samson, mu yi masa kamar yadda ya yi mana.”

11. Sa'an nan mutum dubu uku na Yahuza suka gangara zuwa kogon dutsen Itam. Suka ce wa Samson, “Ba ka sani ba Filistiyawa ne suke mulkinmu? Me ya sa ka yi mana haka?”Shi kuwa ya amsa musu, ya ce, “Kamar yadda suka yi mini, haka ni kuma na yi musu.”

12. Suka ce masa, “Mun gangara zuwa wurinka don mu ɗaure ka, mu miƙa ka gare su.”Samson ya ce musu, “Ku rantse mini idan ba ku ne da kanku kuke so ku kashe ni ba.”

13. Suka ce masa, “A'a, ba za mu kashe ka ba, mu dai za mu kama ka, mu miƙa ga Filistiyawa.” Sa'an nan suka ɗaure shi da sababbin igiyoyi biyu, suka sauko da shi daga dutsen.

14. Sa'ad da ya zo Lihai, sai Filistiyawa suka sheƙo a guje suna ihu suka nufo shi. Ruhun Ubangiji ya sauko kansa da iko, sai igiyoyin da suke a ɗaure da shi suka tsintsinke kamar zaren da ya kama wuta.

15. Ya kuwa sami sabon muƙamuƙin jaki, ya ɗauka ya kashe mutum dubu da muƙamuƙin.

16. Sa'an nan Samson ya raira waƙa ya ce.“Da muƙamuƙin jaki na kashe mutum dubu,Da muƙamuƙin jaki na tsiba su tsibi-tsibi.”

17. Da ya gama, ya jefar da muƙamuƙin. Sai aka ba wurin suna, Ramat-Lihai, wato tudun muƙamuƙi.

18. Ƙishirwa kuwa ta kama shi ƙwarai, sai ya roƙi Ubangiji ya ce, “Kai ne ka yi wannan babbar nasara ta hannun bawanka, yanzu kuwa ko zan mutu da ƙishirwa, har Filistiyawa marasa kaciya su kama ni?”

19. Allah kuwa ya buɗe wani rami daga ƙasa, sai ruwa ya ɓuɓɓugo daga ciki. Da ya sha, hankalinsa ya komo, ya wartsake. Don haka aka ba wurin suna En-hakkore, wato mai kira. Ramin yana nan a Lihai har wa yau.

20. Samson ya shugabanci Isra'ilawa shekara ashirin a zamanin da Filistiyawa suke mulkinsu.

Karanta cikakken babi L. Mah 15