Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Mah 12:7-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Yefta mutumin Gileyad ya shugabanci Isra'ilawa shekara shida, sa'an nan ya rasu. Aka binne shi a garinsu, wato Gileyad.

8. Bayan Yefta, sai Ibzan, mutumin Baitalami ya shugabanci Isra'ilawa.

9. Yana da 'ya'ya maza talatin, da 'ya'ya mata talatin. Ya aurar da 'ya'yansa mata ga wata kabila, ya kuma auro wa 'ya'yansa maza 'yan mata daga wata kabila. Ya shugabanci Isra'ilawa shekara bakwai.

10. Sa'an nan ya rasu, aka binne shi a Baitalami.

11. Bayansa kuma, sai Elon mutumin Zabaluna ya shugabanci Isra'ilawa shekara goma.

12. Sa'an nan ya rasu, aka binne shi a Ayalon a ƙasar Zabaluna.

13. Bayan Elon kuma, sai Abdon, ɗan Hillel, mutumin Firaton, ya shugabanci Isra'ilawa.

14. Yana da 'ya'ya maza arba'in, da jikoki maza talatin, suna hawan jakai saba'in. Abdon ya shugabanci Isra'ilawa shekara takwas.

15. Sa'an nan ya rasu, aka binne shi a Firaton ta ƙasar Ifraimu a tudun Amalekawa.

Karanta cikakken babi L. Mah 12