Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Mah 12:6-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. sai su ce masa, to, ka ce, “Shibbolet,” sai mutum ya ce, “Sibbolet,” gama ba ya iya faɗa daidai. Sai su kama shi su kashe a mashigan Urdun. Mutanen Ifraimu da aka kashe a lokacin su dubu arba'in da dubu biyu (42,000) ne.

7. Yefta mutumin Gileyad ya shugabanci Isra'ilawa shekara shida, sa'an nan ya rasu. Aka binne shi a garinsu, wato Gileyad.

8. Bayan Yefta, sai Ibzan, mutumin Baitalami ya shugabanci Isra'ilawa.

9. Yana da 'ya'ya maza talatin, da 'ya'ya mata talatin. Ya aurar da 'ya'yansa mata ga wata kabila, ya kuma auro wa 'ya'yansa maza 'yan mata daga wata kabila. Ya shugabanci Isra'ilawa shekara bakwai.

10. Sa'an nan ya rasu, aka binne shi a Baitalami.

11. Bayansa kuma, sai Elon mutumin Zabaluna ya shugabanci Isra'ilawa shekara goma.

Karanta cikakken babi L. Mah 12