Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Mah 1:24-35 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. Sai 'yan leƙen asirin ƙasar suka ga wani mutum yana fitowa daga cikin birnin, suka ce masa, “Muna roƙonka ka nuna mana hanyar shiga birnin, mu kuwa za mu yi maka alheri.”

25. Ya kuwa nuna musu, suka shiga suka kashe dukan mutanen birnin, amma suka bar mutumin da iyalinsa duka.

26. Sai mutumin ya tafi ƙasar Hittiyawa, ya gina birni, ya sa masa suna Luz, haka ake kiran birnin har wa yau.

27. Kabilar Manassa ba su kori waɗanda suke zaune a Bet-sheyan, da Ta'anak, da Dor, da Ibleyam, da Magiddo, da garuruwan da suke kusa da su ba, amma Kan'aniyawa suka yi kanekane cikin ƙasar.

28. Sa'ad da Isra'ilawa suka yi ƙarfi, suka sa Kan'aniyawa su yi aikin gandu, amma ba su kore su ba.

29. Mutanen Ifraimu kuma ba su kori Kan'aniyawan da suke zaune cikin Gezer ba, amma Kan'aniyawa suka yi zamansu a Gezer tare da su.

30. Mutanen Zabaluna ma ba su kori mazaunan Kattat da na Nahalal ba, amma Kan'aniyawa suka zauna tare da su, suna yi musu aikin gandu.

31. Haka kuma mutanen Ashiru ba su kori mazaunan Akko, da na Sidon, da Alab, da Akzib, da Helba, da Afek, da Rehob ba.

32. Amma Ashirawa suka yi zamansu tare da Kan'aniyawan ƙasar, gama ba su kore su ba.

33. Mutanen Naftali ma ba su kori mazaunan Bet-shemesh, da na Bet-anat ba, amma suka zauna tare da Kan'aniyawan ƙasar, duk da haka mazaunan Bet-shemesh da na Bet-anat suka zama masu yi musu aikin gandu.

34. Amoriyawa suka matsa wa Danawa, suka angaza su cikin ƙasar tuddai, ba su yarda musu su zauna a filayen ba.

35. Amoriyawa kuwa suka nace su zauna a Heres, da Ayalon, da Shalim. Amma mutanen kabilar Yusufu suka mallake su har suka zama masu yi musu aikin gandu.

Karanta cikakken babi L. Mah 1