Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Mah 1:18-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Yahuza kuma ya ci Gaza da karkararta, da Ashkelon da karkararta, da Ekron da karkararta.

19. Ubangiji kuwa yana tare da Yahuza, ya mallaki ƙasar tuddai, amma bai iya korar waɗanda suke zaune a fili ba, domin suna da karusan ƙarfe.

20. Aka ba Kalibu Hebron kamar yadda Musa ya faɗa. Shi kuwa ya kori 'ya'yan Anak, maza, su uku, a can.

21. Amma mutanen Biliyaminu ba su kori Yebusiyawan da suke zaune a Urushalima ba domin haka Yebusiyawa suka yi zamansu tare da mutanen Biliyaminu a Urushalima har wa yau.

22. Jama'ar kabilar Yusufu kuwa suka haura don su yaƙi Betel, Ubangiji kuwa yana tare da su.

23. Suka aika a leƙi asirin Betel wadda a dā ake kira Luz.

24. Sai 'yan leƙen asirin ƙasar suka ga wani mutum yana fitowa daga cikin birnin, suka ce masa, “Muna roƙonka ka nuna mana hanyar shiga birnin, mu kuwa za mu yi maka alheri.”

25. Ya kuwa nuna musu, suka shiga suka kashe dukan mutanen birnin, amma suka bar mutumin da iyalinsa duka.

26. Sai mutumin ya tafi ƙasar Hittiyawa, ya gina birni, ya sa masa suna Luz, haka ake kiran birnin har wa yau.

Karanta cikakken babi L. Mah 1